Duniyar Aljanu

Duniyar Aljanu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Duniyar Aljanu, Media/News Company, Wuse Zone 3, Englewood, NJ.

08/19/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Malam Mai Yasin, Ahmad Muhammad

IRIN ILLAR DA UMMUL AƊFAL KE YIWA YARA.                             1-Suna ɗaukar jariran mutane su tafi yawo da su, Wan...
06/21/2026

IRIN ILLAR DA UMMUL AƊFAL KE YIWA YARA. 1-Suna ɗaukar jariran mutane su tafi yawo da su, Wani lokaci ma uwar yaron tana kallo za'a ɗauki yaron ayi waje da shi sai ta ringa ganin k**ar a mafarki ne.

2-Suna baiwa yara ruwa ko kuma guba su sha.

3-Suna ɗaukar jariran mutane su ba su nono.

4-Suna zuwa tun lokacin saduwa su yi ƙoƙarin haɗa tsatsonsu dana uban yaron, don a haifo musu ɗa. Da dai sauransu.

YADDA AKE TSARE YARA DAGA SHARRIN UMMUL AƊFAL da yardar Allah.

•A dinga sanyawa yara tufafi idsn za suyi bacci, ma'ana kada a kwantar da su tsirara. Hak**a lokacin da suke harkokinsu da rana.

•A dinga baiwa Jinjiri ruwan zam-zam koda lokaci zuwa lokaci ne.

•A haɗa man Zaitun da Man Habbatussauda a karant ayoyin Rukya a dinga shafewa Yaro jikinsa koda sau ɗaya ne a sati.

•A dinga tofa Ayatal Kursiyyu da Falaqi da Nasi a ruwa ana baiwa yaro yana sha.

YARON DA YA RIGA YA KAMU gaskiya sai an kai
shi wajen Malamai masana harkar Aljanu da magunguna.

ZUWA GA MAI RUƘIYYA Yadda zaka mu'amalanci Aljanin yara wajen fitar da shi.

1-Idan aka ce Aljanin yara ana nufin yaro ɗan shekara goma sha biyu zuwa ƙasa.

2-Yaro jikinsa yana da rauni, don haka ba ko da yaushe Aljani yake zaune a jikinsa ba.

3-Ingantacciyar hanyar cirewa yaro Aljani shi ne a ɗora hannu akan ƙirjinsa ayi masa karatu a kunnensa na dama.

4-A tabbatar an shafewa yaron jikinsa da Man Zaitun wanda aka tofa ayoyin Ruq'yah a ciki kafin a fara yi masa Ruq'yar kuma a nisanci ido da shi domin Man Zaitun yana zafi a ido.

5-Kada a ɗau dogon lokaci ana magana da Aljani a jikin yaro, kawai ayi saurin fitar da shi ta hanya mai sauƙi.

6-Lokacin da za ayi wa yaro Ruq'yah sai ayi amfani da sauti madaidaici yadda yaron ba zai firgita ba.

7-Kada a sanar da yaro ƙarami cewa Aljanu ne suke damunsa. A dai nuna masa kawai wata lalura ce ta daban .

8-Idan Ruq'yah ba aikinka bace, kada ka ce za kayi wa wani yaro ko babba. Zai fi kyau a kai mutum wajen masu aikin.

ALAMOMIN DA ZA'A GANE JINNUL AƊFAL YA SHAFI
YARO :-

1-Yaro ya dinga firgita shi kaɗai yana razana.

2-yaro ya riƙa tsalla kuka da tsakar dare kuma ya ƙi jin rarrashi.

3-Wani lokacin kuma ya kan daƙile jikin yaro ya
hanashi girma, ya hanashi kuzari, Sai dai ƙasusuwan yaro duk sun fiffito k**ar a ƙirga su.

4-Yaro ya zama ba ya dariya ko murmushi idan anyi masa wasa.

5-Yaro ya dinga kallon sama shi kaɗai yana
dariya, Ko kaga yana kallon gefensa k**ar ana ɗaukar hankalinsa.

6-Yakan sa yaro ya dinga kallon-ruwa (wato
idonsa ya wurƙile). ƙwayoyin idonsa su juye

7-Galibin yaran s**an zama masu ƙaton kai da
siraran ƙafafuwa (idan abin yayi ƙarfi).

9-Wani lokaci idan Babarsa ta haɗa jiki da shi sai
ta ji k**ar wani abu yana yi ma ta 'yummm ' a jikinta.

10-Yaro ya kan zama mai faɗa da cizon yaran mutane.

11-Yaro yakan zama mara jin magana kuma baya
jin duka, ba ya rabuwa idan suna faɗa.

12-Wani yaron sam ba ya magana, wani kuma ba ya fita cikin yara sosai.

13-Ya kan sa yaro ya dinga dalalar da yawu daga bakinsa.

14-Ya kan shanyewa yaro hannu ko ya dinga jan ƙafa.

15-Wani lokaci ya kan bar tabo a jikin yaro, a ga wani abu ya fito masa a kai ko a ciki ko a gadon baya.

16-Yakan riƙewa yaro ƙafa ya hana shi tafiya.

17-Ya kan sa kan yaro ya ƙi tsayawa.

18-Yana sa gashin kan yara ya dinga ciccizgewa, ko kuma su dinga tsigewa da hannunsu.

19-Yana sa yaro ya zama dolo a cikin yara.

20-Yana sa yaro ya dinga ɗauke-ɗauken kayan
mutane ko kuɗi.

Da dai alamomi masu yawa.

Indai Yaro ya girma da wannan Aljani a jikinsa ba'a cire mishi tun yana ƙarami ba to yana da wahala su rabu da shi, sai an dage, domin kuwa ko Ruƙiyya akayi ba sa magana, wani lokacin kuma su kan yi magana da ƙyar. Kuma ba su fiye rabuwa da shi kwata-kwata ba, sai dai suyi sauƙi.

Idan wannan Aljani ya girma tare da yaro ya kan
zamar ma sa JINNUL QARIYN ﺟﻦ ﺍﻟﻘﺮﻳﻦ wanda muka yi bayanin sa.

YARON DA YA RIGA YA KAMU gaskiya sai an kai
shi wajen Malamai masana harkar Aljanu da magunguna.

ZUWA GA MAI RUƘIYYA Yadda zaka mu'amalanci Aljanin yara wajen fitar da shi.

1-Idan aka ce Aljanin yara ana nufin yaro ɗan shekara goma sha biyu zuwa ƙasa.

2-Yaro jikinsa yana da rauni, don haka ba ko da yaushe Aljani yake zaune a jikinsa ba.

3-Ingantacciyar hanyar cirewa yaro Aljani shi ne a ɗora hannu akan ƙirjinsa ayi masa karatu a kunnensa na dama.

4-A tabbatar an shafewa yaron jikinsa da Man Zaitun wanda aka tofa ayoyin Ruq'yah a ciki kafin a fara yi masa Ruq'yar kuma a nisanci ido da shi domin Man Zaitun yana da. zafi a cikin ido.

5-Kada a ɗau dogon lokaci ana magana da Aljani a jikin yaro, kawai ayi saurin fitar da shi ta hanya mai sauƙi.

6-Lokacin da za ayi wa yaro Ruq'yah sai ayi amfani da sauti madaidaici yadda yaron ba zai firgita ba.

7-Kada a sanar da yaro ƙarami cewa Aljanu ne suke damunsa. A dai nuna masa kawai wata lalura ce ta daban .

8-Idan Ruq'yah ba aikinka bace, kada ka ce za kayi wa wani yaro ko babba. Zai fi kyau a kai mutum wajen masu aikin.

9-Idan aka yi wa Yaro ƙarami ɗan ƙasa da shekara huɗu Ruƙiyya zai iya mutuwa, Amma anayi idan kwararre ne a harkar Ruqya.

Ya Allah Ka tsare mana lafiyar mu da ta 'ya'yanmu,
waɗanda s**a kamu kuma Allah Ka ba su lafiya.

Masu kallo da sauraro da bibiyar Shafukan mu na kafafen sada zumunta na internet, Zamu dakata a nan. Sai shiri na gaba zamu tashi a kan JINNUT_TABADDUL
Nau'in Aljanun da ba sa mutuwa.

•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••
Daga Cibiyar Binciken Cututtuka da Magungunan Musulunci da Nazarin rayuwar Halittar Aljanu da Sihiri da bayar da Shawarwari dangane da Cututtuka na fili da na boye, ta AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Domin neman shawara ko ƙarin bayani Zaku iya ziyartar mu a ofishin mu dake,

Abuja Office:
Address No, 4th Floor Amac Plaza opp Heritage House Wuse Zone 3 FCT Abuja.

Kano Office:
No 5 Naibawa Dan Hassan Street off Masallacin Juma'a na Quba, Naibawa Kano.

Zaku iya bibiyar mu ta shafukan mu k**ar haka:
AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE

✓FACEBOOK ✓WHATSAPP ✓TELEGRAM ✓X TWITTER
✓INSTAGRAM ✓YOUTUBE
✓TIKTOK ✓WEBSITE

24/7 INTERNET SERVICES

FACEBOOK PAGE
Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin.
https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

WHATSAPP GROUP
Za'a iya yin joint da shafin mu na whatsapp domin samun damar shiga group.

https://chat.whatsapp.com/GVO71jLDmvX29uxAbwIeMv

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/+IDjk1C3K3kdhZDI0

Haka kuma muna turawa da Magungunan mu a ko ina ne a faɗin duniya.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••

UMMUL_AƊFAL_أم_ألالطفالAljanar Jarirai.Aljana mai shiga jikin ƙananan yara.Ummul Aɗfal ﺍﻡ ﺍﻻﻃﻔﺎﻝ                    ko k...
06/21/2026

UMMUL_AƊFAL_أم_ألالطفال

Aljanar Jarirai.
Aljana mai shiga jikin ƙananan yara.
Ummul Aɗfal ﺍﻡ ﺍﻻﻃﻔﺎﻝ ko kuma Inna Uwa a Hausance.

•┈━━━•❄︎• ﷽ •❄︎•━━━┈•
MASU KALLO DA MASU SAURARON MU DA MASU BIBIYAR MU TA SHAFUKAN MU NA KAFAFEN SADA ZUMUNTA NA INTERNET, ASSALAMU ALAIKUM.

BARKAN MU DA SAKE KASANCEWA TARE DAKU TA CIKIN WANNAN SHIRI NA SAUTUL MANARUSH-SHIFA.

MUNA NAN A CIKIN DUNIYAR ALJANU, Muna bayani ne dai dangane da Duniyar Aljanu da abin da ta kunsa.
•═════❀🏮❀══════•

اعوذبالله من الشيطان الرجيم
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ

A cigaba da kawo muku bayanai akan Nau'o'in Aljanu da Rabe-rabensu da kuma irin Cututtukan da suke sakawa mutane da Magungunansu, yau insha Allahu za muyi bayani ne a kan Ummul Aɗfaal, Aljana mai shiga jikin Jariran mutane.

MANZO SAW YACE:
ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ.
ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﺭﻭﺡ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺩﺓ . ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﺑﻦ ﺟﺮﻳﺞ . ﺃﺧﺒﺮﻧﻲ ﻋﻄﺎﺀ؛ ﺃﻧﻪﺳﻤﻊ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻳﻘﻮﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ: ( ﺇﺫﺍ ﺟﻨﺢ ﺍﻟﻠﻴﻞ - ﺃﻭﺃﻣﺴﻴﺘﻢ - ﻓﻜﻔﻮﺍ ﺻﺒﻴﺎﻧﻜﻢ. ﻓﺈﻥﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻳﻨﺘﺸﺮ ﺣﻴﻨﺌﺬ . ﻓﺈﺫﺍﺫﻫﺐ ﺳﺎﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻓﺨﻠﻮﻫﻢ. ﻭﺃﻏﻠﻘﻮﺍ ﺍﻷﺑﻮﺍﺏ . ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢﺍﻟﻠﻪ. ﻓﺈﻥ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻻ ﻳﻔﺘﺢ ﺑﺎﺑﺎ
ﻣﻐﻠﻘﺎ. ﻭﺃﻭﻛﻮﺍ ﻗﺮﺑﻜﻢ. ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ. ﻭﺧﻤﺮﻭﺍ ﺁﻧﻴﺘﻜﻢ.ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ. ﻭﻟﻮ ﺃﻥﺗﻌﺮﺿﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺷﻴﺌﺎ. ﻭﺃﻃﻔﺆﺍﻣﺼﺎﺑﻴﺤﻜﻢ

Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Ya ce: "Idan dare ya shiga ko kuma kun yamma ta, to ku kame ƙananan "YA"YANKU, domin awannan lokacin ne shaiɗanu suke yaɗuwa, amma idan aka sami kimanin awa ɗaya to kwa iya sakin yaranku. kuma idan zaku kwanta ku rufe ƙofofinku, idan zaku rufe ku ambaci sunan ALLAH. domin Shaiɗan ba ya iya buɗe ƙofar da aka rufe ta (da sunan Allah).

Kuma ku kife ƙorukan ku. (jam'in QWARYA) Ku ambaci sunan ALLAH yayin da zaku kife, kuma ku rufe tukwanan ku, ku ambaci ALLAH lokacin da zaku rufe ɗin, ko da wani abu ne ku ɗora akai, kuma idan zaku kwanta bacci ku kashe fitila" (sahih Muslim)

Daga wannan hadisi za mu fahimci cewa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Yana umartarmu mu kame yaran mu mu kula da su a dai dai lokacin da Shaiɗanu suke yaɗuwa don kada su shafe su.

ABUBUWAN DA SUKE SA UMMUL AƊFAL TA SHIGA JIKIN YARA

✍🏻Daga Shafin AL-manar Islamic Medicine, masu yin Ruq'yah da har-haɗa magungunan Musulunci.

Shiga shafinmu na facebook a cikin wannan shuɗin rubutun sai ka danna like,

Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin.
https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Idan muka ce Ummul Aɗfal muna nufin nau'in Aljanun da ke shiga jikin ƙananan yara. Aljanun suna iya kasancewa Maza ne ko kuma mata, Amma dai mafi yawansu mata ne, Shi ya sa ma ko a Hausa idan Aljani ya k**a yaro sai a ce INNA UWA ce a jikinsa, ko ace SHAN INNA.
To abubuwan da ke kawo wannan Aljana jikin yara suna da yawa, k**ar:-

1-GADO. Idan ya kasance mahaifiya ta yi lalurar Aljanu lokacin da take da ciki, to zata iya haifo yaro mai lalurar Aljanu.

2-Idan ya kasance gidan da suke zaune a ciki wajen zaman Aljanu ne, to za su iya shafar yaron.

3-Barin yara suna bacci ko suna yawo tsirara ba sutura a jikinsu.

4-Barin yara suna yawo da Magriba, k**ar yadda ya zo a Hadisin da muka kawo.

5-Barin yara suna wasa a guraren zaman Aljanu k**ar Banɗaki ko wajen shara ko bola ko kuma shuri. (Shuri wani gurin zaman aljanu ne dake fitowa a daji ko kuma wani lokacin yana fitowa a gida musamman ɗakin da ba'a amfani dashi.)

6-Rashin yiwa yara addu'a yayin da za su kwanta bacci ko kuma sauran harkokin rayuwa.

7-Yi wa yara kwalliya irinta Shaiɗanu da dai sauransu.

ALAMOMIN DA ZA A GANE JINNUL AƊFAL YA SHAFI
YARO :-

1-Yaro ya dinga firgita shi kaɗai yana razana.

2-yaro ya riƙa tsalla kuka da tsakar dare kuma ya ƙi jin rarrashi.

3-Wani lokacin kuma ya kan daƙile jikin yaro ya
hanashi girma, ya hanashi kuzari, Sai dai ƙasusuwan yaro duk sun fiffito k**ar a ƙirga su.

4-Yaro ya zama ba ya dariya ko murmushi idan anyi masa wasa.

5-Yaro ya dinga kallon sama shi kaɗai yana dariya. Ko kaga yana kallon gefensa k**ar ana
ɗaukar hankalinsa.

6-Yakan sa yaro ya dinga kallon-ruwa (wato
idonsa ya wurƙile). ƙwayoyin idonsa su juye

7-Galibin yaran s**an zama masu ƙaton kai da
siraran ƙafafuwa (idan abin yayi ƙarfi).

9-Wani lokaci idan mamansa ta haɗa jiki da shi sai ta ji k**ar wani abu yana yimata 'yummm a jikinta.

10-Yaro ya kan zama mai faɗa da cizon yaran mutane.

11-Yaro yakan zama mara jin magana kuma baya jin duka, ba ya rabuwa idan suna faɗa.

12-Wani yaron sam ba ya magana, wani kuma ba
ya fita cikin yara sosai.

13-Ya kan sa yaro ya dinga dalalar da yawu daga bakinsa.

14-Ya kan shanyewa yaro hannu ko ya dinga jan ƙafa.

15-Wani lokaci ya kan bar tabo a jikin yaro, a ga wani abu ya fito masa a kai ko a ciki ko a gadon baya.

16-Yakan riƙewa yaro ƙafa ya hana shi tafiya.

17-Ya kan sa kan yaro ya ƙi tsayawa.

18-Yana sa gashin kan yara ya dinga ciccizgewa, ko kuma su dinga tsigewa da hannunsu.

19-Yana sa yaro ya zama dolo a cikin yara.

20-Yana sa yaro ya dinga ɗauke-ɗauken kayan
mutane ko kuɗi.

Da dai alamomi masu yawa.

Indai Yaro ya girma da wannan Aljani a jikinsa ba'a cire mishi tun yana ƙarami ba to yana da wahala su rabu da shi, sai an dage.

Domin kuwa ko Ruƙiyya akayi ba sa magana, wani lokacin kuma su kan yi magana amma daƙyar. Kuma ba su fiye rabuwa da shi kwata-kwata ba, sai dai suyi sauƙi.

Idan wannan Aljani ya girma tare da yaro ya kan
zamar masa JINNUL QARIYN ﺟﻦ ﺍﻟﻘﺮﻳﻦ wanda muka yi bayaninsa a baya.

Masu kallo da sauraro da bibiyar Shafukan mu na kafafen sada zumunta na internet, Zamu dakata a nan, sai a shiri na gaba inda zamu tashi kan IRIN ILLAR DA UMMUL AƊFAL KE YIWA YARA.

•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••
Daga Cibiyar Binciken Cututtuka da Magungunan Musulunci da Nazarin rayuwar Halittar Aljanu da Sihiri da bayar da Shawarwari dangane da Cututtuka na fili da na boye, ta AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Domin neman shawara ko ƙarin bayani Zaku iya ziyartar mu a ofishin mu dake,

Abuja Office:
Address No, 4th Floor Amac Plaza opp Heritage House Wuse Zone 3 FCT Abuja.

Kano Office:
No 5 Naibawa Dan Hassan Street off Masallacin Juma'a na Quba, Naibawa Kano.

Zaku iya bibiyar mu ta shafukan mu k**ar haka:
AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE

✓FACEBOOK ✓WHATSAPP ✓TELEGRAM ✓X TWITTER
✓INSTAGRAM ✓YOUTUBE
✓TIKTOK ✓WEBSITE

24/7 INTERNET SERVICES

FACEBOOK PAGE
Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin. https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

WHATSAPP GROUP
Za'a iya yin joint da shafin mu na whatsapp domin samun damar shiga group.

https://chat.whatsapp.com/GVO71jLDmvX29uxAbwIeMv

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/+IDjk1C3K3kdhZDI0

Haka kuma muna turawa da Magungunan mu a ko ina ne a faɗin duniya.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••

AMIRUL BAYTI   ِﻋﺎﻣﺮُ ﺍﻟﺒَﻴٗﺖKo kuma Khadimul Manzil خادم المنزلAljanin gida.Aljanun da suke maƙale  suke zaune a gidaje...
06/21/2026

AMIRUL BAYTI ِﻋﺎﻣﺮُ ﺍﻟﺒَﻴٗﺖ
Ko kuma Khadimul Manzil خادم المنزل
Aljanin gida.

Aljanun da suke maƙale suke zaune a gidajen mutane. sune a cikin su ake samun Malam Alhaji su dinga kawowa mutanen gidan kayayyaki k**ar turare ko wasu abubuwan amfani.

•┈━━━•❄︎• ﷽ •❄︎•━━━┈•
MASU KALLO DA MASU SAURARON MU DA MASU BIBIYAR MU TA SHAFUKAN MU NA KAFAFEN SADA ZUMUNTA NA INTERNET, ASSALAMU ALAIKUM.

BARKAN MU DA SAKE KASANCEWA TARE DAKU TA CIKIN WANNAN SHIRI NA SAUTUL MANARUSH-SHIFA.

MUNA NAN A CIKIN DUNIYAR ALJANU, Muna bayani ne dai dangane da Duniyar Aljanu da abin da ta kunsa.
•═════❀🏮❀══════•

Masu bibiyarmu da fatan Kuna binmu sau da kafa, a Shirin da ya gabata mun ƙarƙare labarin JINNUL SHU'UN. yanzu Kuma gamu da labarin wani Shaiɗanin Mai Suna AMEERUL BAYTI.

Su waɗannan wasu nau‘i ne na Aljnu da su ke zaune tare da mutane a cikin gida.

Galibinsu dama can suna zaune ne iyaye da kakanninsu tun wajen yana daji, don haka koda an gina wajen ya zama gida sai su ci gaba da zama tare da mutanen gidan.

✍🏻Daga Shafin AL-manar Islamic Medicine, masu yin Ruq'yah da har-haɗa magungunan Musulunci.

Shiga shafinmu na facebook a cikin wannan shuɗin rubutun sai ka danna like,

Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin.
https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Su waɗannan nau‘in Aljanu suna tasirantuwa ne da irin abinda mutanen gida suke aikatawa. Misali idan mutanen gidan suna sallah to su ma za su yi sallah tare da su ko karatun Alqur‘ani. Idan kuma mutanen suna jin kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe to su ma sai ya zama wannan su ke so.

ABUBUWAN DA KE KAWO ALJANU CIKIN GIDA

•Barin gida ba mutane a ciki tsawon shekaru ko watanni.

•Barin wani ɗaki a cikin gida ba kowa a ciki, to Aljanu za su tare a ciki.

•Yawan kunna kaɗe-kaɗe a cikin gida.

•Ajiye abubuwan Shaiɗanu a gida, k**ar gumaka, kayan tsafe tsafe ko karnuka.

•Rashin karatun Alqur'ani a cikin gida.

•Yin shaye-shayen kayan maye ko zinace zinace a gida.

•Zuzzubar da abinci ko abin sha a ƙasa.

•Barin gida da ƙazanta da tarin shara ko bola (Juji).

•Gina gida a kan shuri. Da dai sauransu.

YADDA ZA A GANE AKWAI AMEERUL BAITI A CIKIN GIDAN MUTANE :-

Yawan jin sallama ko takun ƙafafu ba tare da an ga kowa ba.

Yawan ganin wani mutum ko mace zaune a cikin gida ko banɗaki.

Yawan ɓatan kaya kuma a rasa wanda ya ɗauka, sai lokacin da ba ka buƙatarsa kuma sai ka gan shi.

Yawan ganin an hargitsa ma ka kaya ko anyi maka bincike kuma ka rasa ko waye.

Yawan ɓacin rai ko faɗuwar gaba idan kana cikin gida amma idan ka fita sai ka daina ji.

Yawan tsagewar wata katanga a cikin gida kuma duk gyaran da za'a yi sai ta kuma darewa.

Yawan ganin wata dabba ta gifta k**ar maciji ko kare etc. kuma idan an duba sai a rasa inda ya shiga.

Yawan jin dudubniya ko kokaye-kokaye a saman ɗaki.

YADDA AKE KORAR WANNAN ALJANI DAGA CIKIN GIDA:-

A dinga karanta Suratul Baqarah duk bayan kwana uku a gidan, ko a dinga kunnawa a kaset ko mp ko Handset.

Idan kuma ba su fita ba to sai a nemo mai ruƙiyya ya yi magana dasu ya sallamesu.

Masu kallo da sauraro da bibiyar Shafukan mu na kafafen sada zumunta na internet, Zamu dakata a nan. Kuma nan muka kawo ƙarshen labarin AMEERUL BAYTI. a shiri na gaba zamu tashi da labarin UMMUL ADFAL (ALJANAR DA TAKE BIBIYAR YARA.

•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••
Daga Cibiyar Binciken Cututtuka da Magungunan Musulunci da Nazarin rayuwar Halittar Aljanu da Sihiri da bayar da Shawarwari dangane da Cututtuka na fili da na boye, ta AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Domin neman shawara ko ƙarin bayani Zaku iya ziyartar mu a ofishin mu dake,

Abuja Office:
Address No, 4th Floor Amac Plaza opp Heritage House Wuse Zone 3 FCT Abuja.

Kano Office:
No 5 Naibawa Dan Hassan Street off Masallacin Juma'a na Quba, Naibawa Kano.

Zaku iya bibiyar mu ta shafukan mu k**ar haka:
AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE

✓FACEBOOK ✓WHATSAPP ✓TELEGRAM ✓X TWITTER
✓INSTAGRAM ✓YOUTUBE
✓TIKTOK ✓ WEBSITE

24/7 INTERNET SERVICES

FACEBOOK PAGE
Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin. https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

WHATSAPP GROUP
Za'a iya yin joint da shafin mu na whatsapp domin samun damar shiga group.

https://chat.whatsapp.com/GVO71jLDmvX29uxAbwIeMv

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/+IDjk1C3K3kdhZDI0

Haka kuma muna turawa da Magungunan mu a ko ina ne a faɗin duniya.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••

YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUL SHU'UN YA SHAFE SHI.•┈━━━•❄︎• ﷽ •❄︎•━━━┈•MASU KALLO DA MASU SAURARON MU DA MASU BIBIYAR MU T...
06/21/2026

YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUL SHU'UN YA SHAFE SHI.
•┈━━━•❄︎• ﷽ •❄︎•━━━┈•
MASU KALLO DA MASU SAURARON MU DA MASU BIBIYAR MU TA SHAFUKAN MU NA KAFAFEN SADA ZUMUNTA NA INTERNET, ASSALAMU ALAIKUM.

BARKAN MU DA SAKE KASANCEWA TARE DAKU TA CIKIN WANNAN SHIRI NA SAUTUL MANARUSH-SHIFA.

MUNA NAN A CIKIN DUNIYAR ALJANU, Muna bayani ne dai dangane da Duniyar Aljanu da abin da ta kunsa.
•═════❀🏮❀══════•
YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUL SHU'UN YA SHAFE SHI.

Masu bibiyarmu a wannan Shirin Allah Yasa Kuma Jin dadin labarurruka da muke bayarwa, har yanzu Muna nan a labarin JINNUL SHU'UN,

✍🏻Daga Shafin AL-manar Islamic Medicine, masu yin Ruq'yah da har-haɗa magungunan Musulunci.

Shiga shafinmu na facebook a cikin wannan shuɗin rubutun sai ka danna like,

Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin.
https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.
★ Wani lokacin mutum yana tafiya sai ya ga wani ɗan mitsitsin mutum bai fi a kife shi da ƙwarya ba, Kuma sai ya tsaya ya ƙura maka ido ko yayi maka magana, Idan ka ji tsoro ko ka gudu shikenan sai ya shiga jikinka.

★Wani lokacin za ka hango mutum yana tahowa wajenka daga nesa amma sai ka ga ya daɗe sai tahowa yake kuma bai ƙaraso ba, Daga baya sai ka ga ba komai kuma ya ɓace.

★Haka kawai sai mutum yaga inuwa tana bin sa, Idan ya waiwaya kuma ba zai ga komai ba. Ko mutum ya ga k**ar wani abu ya gifta ta kusa da shi. Wani lokacin ma mutum zai ji k**ar ana bin sa a baya ko ya dinga jin motsi a kusa da shi amma dai duk ba zai ga kowa ba.

★Jin k**ar ana kiranka amma baka ga kowa ba, Za ka ji an kira sunan ka miraran amma sai ka duba baka ga kowa ba, wani lokacin ma da muryar wanda ka sani amma idan ka tambaye shi zai ce shi bai kiraka ba.

★Yawan ɓacewar abu sai daga baya a gan shi. Mutum zai ajiye abinsa amma yayi ta nemansa bai gan shi ba har sai ya gaji ya haƙura sai kuma ya gan shi a kusa da shi.

★Za ka ga babban mutum ko kuma matashi amma yana magana irin ta yara ko kuma yana ayyuka da wasanni tare da yara kuma irin na yara. Kamar shaɓune ko saɓalikita ko dalalau da dai sauransu.

★Mutum zai zama mai yawan shirme. Ga shi dai ya kai lokacin da ya k**ata hankalinsa ya cika amma kuma yana abubuwan shirme.

★Masu matsalar Jinnul Shu'un ba za su taɓa yarda cewa basu da hankali ba. Domin idan ka ce musu mahaukata za ku iya yin faɗa, idan kuma ka ce musu masu hankali ka san akwai matsala.

★Jinnul Shu'un suna sa mutum ya dinga jin ya fi kowa, Za ka ga mutum ko wanka baya yi amma kuma ba zai gaisa da kai ba saboda yana jin shi ya fi ka.

★ Irin waɗannan mutanen ba a fiye saurin gane su ba sai hira tayi tsawo tukuna. Don wani lokacin za suyi maka shirme wani lokacin kuma suyi magana ta hankali.

★Yaran da Jinnul Shu'uwn ya shafa za ka samu suna da qiriniya sosai da giggiwa. Kuma suna da kazar-kazar da jan faɗa.

★Masu Jinnul Shu'uwn yawanci s**an yi fama da ciwon ƙafa. Musamman tafin ƙafarsu zai dinga yi musu zugi ko ƙafar ta dinga riƙewa.

★Indai mutum yana da Jinnul Shu'uwn to zai dinga yawan cewa an raina masa hankali. Ko ya dinga nuna shi bai yarda da raini ba.

Da dai alamomi da yawa.

YADDA MAI RUQIYYAH ZAI GANE JINNUL SHU'UN NE A JIKIN MUTUM.

★Za ka ga Aljanin yana kallonka ta gefen ido.

★Duk inda hannunka yayi Aljanin zai dinga bin ka da kallo don yaga abinda za ka ɗauko na magani.

★ Kana ɗauko magani ko in zaka fara karatu sai Aljanin ya fara ba ka haƙuri ya ce zai fita.

★Kana cikin yin karatun sai kaga mutum ya miƙe ƙafarsa. Shikenan sai Aljanin ya gudu.

★ Jinnul Shu'un yana da wayo. Zai maka ƙarya ya ce ya fita amma kuma zai ci gaba da magana da kai.

Misali, zai ce na tafi. Sai kuma ka ji yana cewa 'Kalli ma idona ka gani, wallahi na fita. Ka gani?, wallahi ba a jikinta nake ba'.

★Mafi yawa in ka ji kana karatu Aljani yana bin ka to Jinnul Shu'un ne. Koda yake Jinnul Filusafiy ma suna yin ka.

★Jinnul Shu'un suna da taurin kai kafin su bar jikin mutum domin za suyi ta rainawa mai Ruqiyyar hankali. Har wani lokacin ma a ce ba Aljanu ne a jikin mutum ba.

YADDA ZA KA DAURE JINNUL SHU'UN.

Kusan kowanne nau'in Aljanu suna guduwa lokacin da ake yin Ruqiyyah, To akwai yadda ake ɗaure su k**ar yadda muka daɗe muna yin bayani.

Kowanne nau'in Aljani yadda ake ɗaure shi daban ne amma idan Jinnul Shu'un ne sai ka dafa kansa kuma ka riƙe babban ɗan yatsan ƙafarsa sai ka dinga karanta Ayatal kursiyyu. To insha Allahu ba inda za shi har sai ka sallame shi.

Ana ɗaukar awanni da yawa ana fama da jinnul shu'un lokacin ruƙiyyah kafin ya fita. Don haka kayi ƙoƙari ka taƙaita aikin don kar ya wahalar da kai.

WALLAHU A'ALAM.

Masu kallo da sauraro da bibiyar Shafukan mu na kafafen sada zumunta na internet,
Zamu dakata anan.
Kuma anan muke sanar muku cewa mun kawo ƙarshen labarin JINNUL SHU'UN. a shiri na gaba zamu kawo labarin ALJANI AMIRUL BAYTI
Ko kuma Khadimul Manzil
Aljanin gida.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••
Daga Cibiyar Binciken Cututtuka da Magungunan Musulunci da Nazarin rayuwar Halittar Aljanu da Sihiri da bayar da Shawarwari dangane da Cututtuka na fili da na boye, ta AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Domin neman shawara ko ƙarin bayani Zaku iya ziyartar mu a ofishin mu dake,

Abuja Office:
Address No, 4th Floor Amac Plaza opp Heritage House Wuse Zone 3 FCT Abuja.

Kano Office:
No 5 Naibawa Dan Hassan Street off Masallacin Juma'a na Quba, Naibawa Kano.

Zaku iya bibiyar mu ta shafukan mu k**ar haka:
AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE

✓FACEBOOK ✓WHATSAPP ✓TELEGRAM ✓ X
✓INSTAGRAM ✓YOUTUBE
✓TIKTOK

24/7 INTERNET SERVICES

FACEBOOK PAGE
Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin. https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

WHATSAPP GROUP
Za'a iya yin joint da shafin mu na whatsapp domin samun damar shiga group.

https://chat.whatsapp.com/GVO71jLDmvX29uxAbwIeMv

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/+IDjk1C3K3kdhZDI0

Haka kuma muna turawa da Magungunan mu a ko ina ne a faɗin duniya.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••

JINNUL_SHUUN_جن_الشؤونAljanu_Yan_Rainin_WayoNau'in Aljanu masu raina hankalin mutane.•┈━━━•❄︎• ﷽ •❄︎•━━━┈•MASU KALLO DA ...
06/21/2026

JINNUL_SHUUN_جن_الشؤون
Aljanu_Yan_Rainin_Wayo
Nau'in Aljanu masu raina hankalin mutane.
•┈━━━•❄︎• ﷽ •❄︎•━━━┈•
MASU KALLO DA MASU SAURARON MU DA MASU BIBIYAR MU TA SHAFUKAN MU NA KAFAFEN SADA ZUMUNTA NA INTERNET, ASSALAMU ALAIKUM.

BARKAN MU DA SAKE KASANCEWA TARE DAKU TA CIKIN WANNAN SHIRI NA SAUTUL MANARUSH-SHIFA.

MUNA NAN A CIKIN DUNIYAR ALJANU, Muna bayani ne dai dangane da Duniyar Aljanu da abin da ta kunsa.
•═════❀🏮❀══════•
Jama'a Masu bibiyar wannan shiri sau da kafa, barkan mu da sake saduwa, a Shirin da ya gabata mun ƙarƙare labarin JINNUL_QARIYN ﺟﻦُّ ﺍﻟﻘَﺮِﻳﻦ
Nau'in Aljanu waɗanda kowanne mutum yana da su a jikinsa. Yanzu Kuma zamu shiga cikin rayuwar wani aljani Mai Suna:-
JINNUL_SHUUN_جن_الشؤون
Aljanu_Yan_Rainin_Wayo
Nau'in Aljanu masu raina hankalin mutane.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••
Daga Cibiyar Binciken Cututtuka da Magungunan Musulunci da Nazarin rayuwar Halittar Aljanu da Sihiri da bayar da Shawarwari dangane da Cututtuka na fili da na boye, ta AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Domin neman shawara ko ƙarin bayani Zaku iya ziyartar mu a ofishin mu dake,

Abuja Office:
Address No, 4th Floor Amac Plaza opp Heritage House Wuse Zone 3 FCT Abuja.

Kano Office:
No 5 Naibawa Dan Hassan Street off Masallacin Juma'a na Quba, Naibawa Kano.

Zaku iya bibiyar mu ta shafukan mu k**ar haka:
AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE

✓FACEBOOK ✓WHATSAPP ✓TELEGRAM ✓ X
✓INSTAGRAM ✓YOUTUBE
✓TIKTOK

24/7 INTERNET SERVICES

FACEBOOK PAGE
Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin. https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

WHATSAPP GROUP
Za'a iya yin joint da shafin mu na whatsapp domin samun damar shiga group.

https://chat.whatsapp.com/GVO71jLDmvX29uxAbwIeMv

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/+IDjk1C3K3kdhZDI0

Haka kuma muna turawa da Magungunan mu a ko ina ne a faɗin duniya.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••

Jinnul shu'un su ne nau'in Aljanu mafiya yawa a duniya bayan Jinnut Ɗayyar (wato Aljanu masu tashi sama)

Su Jinnul Shu'un sun kasance mazauna ƙasa ne. Wato suna gina gidaje ne a ƙarƙashin ƙasa su zauna ko a cikin ramuka,
Kuma sun kasance suna da cakuɗuwa sosai da mutane k**ar yadda Jinnul ɗayyar suke, Sai dai babu wata cikakkiyar jituwa a tsakaninsu, kasancewar Jinnut Ɗayyar sun fi yin ƙawance ne da Jinnul Gawwas (wato Aljanu mazauna cikin ruwa).

Allah Ya halicci Jinnul Shu'uwn ne da ɗan ƙaramin jiki, Domin gaba ɗaya tsawonsu kaɗan ya wuce idon sawun mutum, Sai dai tafin ƙafarsu yana da girma sosai, Domin tafin ƙafar kawai ya fi gaba ɗayan jikinsu girma,
Suna da manyan kawuna da siraran ƙafafuwa.

Kasancewarsu ƙanana suna da kazar-kazar da ƙiriniya sosai, suna da hanzari da saurin hawa bishiya.

Wannan nau'in Aljanu suna da basira sosai k**ar Jinnul Filosafiy ( Wato Aljanu masu nazarin halayyar Dan Adam).

Jinnul Shu'uwn babu malalaci a cikinsu, domin kowanne wajibi ne ya je yayi sana'a.

A tsarin Sarautar waɗannan Aljanu, dole kowa yayi sana'a sannan kuɗin da ya samo kuma ya kaiwa Sarki.

Shi kuma Sarki yana da masu lura da duk wanda ba ya fita aiki.

Dukkan buƙatunsu na gida da na rashin lafiya Sarki ne yake ɗaukar nauyi kasancewar shi suke kaiwa abinda duk s**a samu.

Ana samun musulmai a cikin Jinnul Shu'un amma a tsarin mulkinsu kowa yana da damar ya bautawa abin da yake so, a gida ɗaya ana iya samun uba musulmi amma ɗansa yana bautawa itace.

Jinnul Shu'uwn suna cikin nau'in Aljanun da suke shiga jikin mutane kuma suna cutar da su sannan suna da raina hankalin mutane.

Ana samun Amirul Baiti a cikinsu ( wato Aljanu masu tarewa a gidan mutane) kuma ana samun Sariqul Jinni a cikinsu (wato Aljanu masu satar kayan mutane).

YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUL SHU'UN YA SHAFE SHI.

Masu kallo da sauraro da bibiyar Shafukan mu na kafafen sada zumunta na internet,
Zamu dakata anan.
sai a shiri na gaba zamu ci gaba da kawo labarin JINNUL SHU'UN.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••
Daga Cibiyar Binciken Cututtuka da Magungunan Musulunci da Nazarin rayuwar Halittar Aljanu da Sihiri da bayar da Shawarwari dangane da Cututtuka na fili da na boye, ta AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE.

Call ☎️+2348162417777.
WhatsApp🪀+2348054583333.

Domin neman shawara ko ƙarin bayani Zaku iya ziyartar mu a ofishin mu dake,

Abuja Office:
Address No, 4th Floor Amac Plaza opp Heritage House Wuse Zone 3 FCT Abuja.

Kano Office:
No 5 Naibawa Dan Hassan Street off Masallacin Juma'a na Quba, Naibawa Kano.

Zaku iya bibiyar mu ta shafukan mu k**ar haka:
AL-MANAR ISLAMIC HEALTH CARE

✓FACEBOOK ✓WHATSAPP ✓TELEGRAM ✓ X
✓INSTAGRAM ✓YOUTUBE
✓TIKTOK

24/7 INTERNET SERVICES

FACEBOOK PAGE
Zaku iya ziyartar shafin mu na Facebook ta wannan link ɗin. https://www.facebook.com/AL-Manar-Islamic-Health-Care-214347695705584/.

WHATSAPP GROUP
Za'a iya yin joint da shafin mu na whatsapp domin samun damar shiga group.
https://chat.whatsapp.com/GVO71jLDmvX29uxAbwIeMv

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/+IDjk1C3K3kdhZDI0

Haka kuma muna turawa da Magungunan mu a ko ina ne a faɗin duniya.
•••━━━━•✿✍🏼✿•━━━━•••

Address

Wuse Zone 3
Englewood, NJ

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar Aljanu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share