05/06/2025
ATIKU FA LOKACI YAYI INSHA ALLAH
Muna kyautata tsammani a yau Talata jagoran siyasarmu a Nigeria Alhaji Atiku Abubakar mai tausayin talakawa zai bayyana matsayarsa game da siyasar 2027 mai karatowa
Muna kyautata zato Atiku da Peter Obi sun fahimci juna, sun amince suyi hadaka domin a ceto Kasar nan daga hannun mutanen da basa tausayin talakawan Nigeria sam
A yanzu Jam'iyyar PDP ta dauko hanyar mutuwa domin shugabanninta Tinubu suke yiwa aiki, duk wani Gwamna ko wani babban dan siyasa da ya bar PDP ya koma APC ya koma ne don neman mafaka akan barnan da yayi ba wai don kishin talakawa ba
A zaben 2023 da ya gabata mafi yawan Gwamnonin PDP ba suyi Atiku ba, mun san Gwamnonin da kwantawa s**ayi lokacin zaben Shugaban Kasa, amma duk da haka ratar dake tsakanin Atiku da Tinubu ba mai yawa bace
Peter Obi ba shi da Gwamna, bashi da Sanata, bashi da dan Majalisar tarayya har mafi karamin mukami wato kansila ko daya bashi da shi a zaben 2023, amma sai da ya samu kuri'u sama da Miliyan 6, yaci jihohi 11 har da birnin tarayya Abuja
A yanzu yadda s**a shirya tsarin cin amanar PDP da kokarin wargaza PDP din, haka mutanen da suke komawa jikinsu zasu ci amanarsa su taimaka wajen kayar da su
Duk abinda Tinubu zai yi walau murdiyan zabe ko amfani da kudi da karfin iko, to da ikon Allah sai Baba Atiku jagoran talakawa da Peter Obi sun kayar da shi a zaben 2027 Insha Allah
Atiku kawai Insha Allah🙏