07/27/2025
RIKICIN MANOMA DA MAKIYAYA
Gwamna Bala Mohammed ya shirya taron tuntuba da ɓangarorin da ke rikici a ƙaramar hukumar Darazo.
Rikice-rikicen da ke yawan faruwa tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Darazo, musamman a wannan lokacin noman bana, sun yi sanadin rasa rayuka da jikkatar mutane da dama.
Idan wannan hali ya ci gaba, ba shakka zai kawo cikas ga harkokin noma na bana. Saboda haka ne Gwamna Bala Mohammed ya ɗauki matakin gaggawa na shirya wannan taron fahimtar juna tare da al’ummomin Fulani da manoma na yankin Darazo.
A lokacin da yake jawabi ga ɓangarorin da ke cikin damuwa, Gwamna Bala Mohammed ya ce zaman lafiya muhimmin ginshiƙi ne na ci gaba. Don haka ya buƙaci su rungumi juna da kuma warware duk wata matsala cikin lumana domin dorewar zaman lafiya da cigaba.
Ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta raba wani ɓangare na dajin Darazo ga 'yan asalin yankin domin amfanin noma bayan bukatar da jama'a s**a gabatar. Amma ya jaddada cewa an tanadi wuraren da dabbobi ke bi (cattle routes) yadda ya k**ata, don haka bai k**ata a taɓa su ba.
Saboda haka, Gwamna Bala Mohammed ya yi kira da a kwantar da hankali, yana mai cewa gwamnati za ta kafa kwamiti na musamman da zai duba dukkan rabon filaye da nufin tabbatar da adalci ga kowa da kowa.
Mutanen da abin ya shafa daga ɓangarorin biyu — manoma da makiyaya — sun bayyana irin abubuwan da ke faruwa a dazukan Yautari, Alia da sauran wurare a Darazo, inda s**a roƙi Gwamna Bala Mohammed da ya kawo musu ɗauki.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bauchi, CP Sani Aliyu, ya jinjina wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan mataki da ya ɗauka. Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro na kan lamarin, tare da gargadin jama'a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
Shugabannin al’umma daga ƙaramar hukumar Darazo da s**a haɗa da 'yan majalisar jiha daga mazabar Darazo da Sade, shugaban ƙaramar hukumar Darazo, hakimin Darazo da ɗan majalisar wakilai na Darazo/Ganjuwa, Mansur Manu Soro — duk sun yaba da kokarin Gwamna Bala Mohammed tare da alkawarin ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Darazo.