12/28/2025
CIKIN SARAKUNAN NIGERIA, KAI NE ALLAH YA BAKA RABO HUDU.
Mai martaba Sarkin Darazo,
Alhaji Ibrahim Babayo Darazo,
sarkin adalci, jagora nagari,
ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kan al’umma,
abin koyi ga matasa, abin alfahari ga dattawa,
haske mai jagorantar masarautar Darazo zuwa alheri.
Ka yi Sardaunan Darazo,
ka yi Mai Gunduma,
ka yi Hakimin Darazo,
ka ratsa dukkan matakan shugabanci cikin gaskiya da rikon amana,
har Allah Ya É—aga ka zuwa matsayin Mai Martaba Sarkin Darazo,
matsayi mai girma da ya dace da hangen nesanka da kyawawan halayenka.
Tun kafin hawanka karagar mulki,
ka kasance mai taimakon talakawa,
mai É—aukar nauyin marasa galihu,
mai sauraron koke-koken jama’a ba tare da nuna bambanci ba.
A yau kuma, kana ci gaba da tafiya a kan tafarkin adalci,
kana fifita zaman lafiya fiye da komai.
Duk abin da ka ƙudura, Allah Ya ma ka,
domin niyyarka tsarkakakkiya ce,
ayyukanka cike suke da gaskiya da tausayi.
Ka riƙe talakawanka da adalci, ladabi da mutunci,
kana haÉ—a zukata, kana sasanta sabani,
kana zama uba ga kowa ba tare da rarrabewa ba.
Duk wanda ya yi ba daidai ba, a gyara masa cikin hikima;
wanda kuma ya yi daidai, a yaba masa a bayyane,
domin hakan shi ne ginshiƙin shugabanci nagari.
Ka ƙarfafa al’ada da addini,
ka kare mutuncin masarauta da martabar Darazo a ko’ina.
Allah Ya ƙara maka hikima da basira,
Ya tsawaita rayuwarka cikin lafiya da natsuwa,
Ya albarkaci mulkinka da zaman lafiya mai É—orewa,
Ya kare ka daga sharrin maƙiya na kusa da na nesa,
Ya sa tarihinka ya zama abin alfahari ga zuri’a mai zuwa.
Masarautar Darazo na alfahari da kai,
jama’a na alfahari da jagorancinka,
kuma Najeriya gaba É—aya na alfahari da irin wannan sarki nagari.
Allah Ya ci gaba da É—aukaka ka,
Ya tabbatar da mulkinka cikin alheri da nasara.
Ameen, Ameen, Ameen. 🤲🤲🤲