Darazo Gida

Darazo Gida Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Darazo Gida, Media/News Company, New G. r. a adamawa, New York, NY.

Page din Darazo Gida Page ne da zaina Kawo Abubuwa Masu Muhimmanci da S**a Shafi Karamar Hukumar Darazo dakuma Bauchi state da Nigeria Gaba daya harma da Abun da Yafita wajen Nigeria

*Ilimantarwa
*Nishadantarwa
*Tallatawa
*Haskawa
Da sauransu

"Ba a kera agogon Casio a matsayin alatu ba, sai dai a matsayin kayan aiki don rayuwa ta har abada. "In ji Tadao Kashio ...
08/08/2025

"Ba a kera agogon Casio a matsayin alatu ba, sai dai a matsayin kayan aiki don rayuwa ta har abada. "In ji Tadao Kashio (mai kamfanin agogo na Casio)

Yayin da wasu masana'antun su ka mayar da hankali kan kera agogon hannu na alatu, Tadao Kashio, wanda ya kafa Casio, ya na da nasa hangen nesa daban, ya kera agogon da zai yi hidima ga ɗalibai, ma'aikata, masana kimiyya, da sauran mutane.

Ya kera agogo mai arha ga kowa da kowa, wanda ba ya bukatar zinariya ko lu'u-lu'u, sai ma'ana kawai. Abin da ya sa Casio ya zama agogo na kowane lokaci.

An kafa kamfanin Casio a cikin shekarar 1946, wanda Tadao Kashio ya kafa. A lokacin, ana kiran kamfanin Kashio Seisakujo. Sai a shekarar 1957 aka canza sunan zuwa Casio Computer Co Ltd. Tadao Kashio injiniya ne, wanda ya kware a fasahar kere-kere.

An haifi Tadao Kashio a ranar 26 ga watan Nuwamba 1917 a Nankoku, Kochi cikin kasar Japan. Ya mutu a ranar 4 ga watan maris 1993 (yana da shekaru 75) a birnin Tokyo na kasar.

RIKICIN MANOMA DA MAKIYAYAGwamna Bala Mohammed ya shirya taron tuntuba da ɓangarorin da ke rikici a ƙaramar hukumar Dara...
07/27/2025

RIKICIN MANOMA DA MAKIYAYA

Gwamna Bala Mohammed ya shirya taron tuntuba da ɓangarorin da ke rikici a ƙaramar hukumar Darazo.

Rikice-rikicen da ke yawan faruwa tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Darazo, musamman a wannan lokacin noman bana, sun yi sanadin rasa rayuka da jikkatar mutane da dama.

Idan wannan hali ya ci gaba, ba shakka zai kawo cikas ga harkokin noma na bana. Saboda haka ne Gwamna Bala Mohammed ya ɗauki matakin gaggawa na shirya wannan taron fahimtar juna tare da al’ummomin Fulani da manoma na yankin Darazo.

A lokacin da yake jawabi ga ɓangarorin da ke cikin damuwa, Gwamna Bala Mohammed ya ce zaman lafiya muhimmin ginshiƙi ne na ci gaba. Don haka ya buƙaci su rungumi juna da kuma warware duk wata matsala cikin lumana domin dorewar zaman lafiya da cigaba.

Ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta raba wani ɓangare na dajin Darazo ga 'yan asalin yankin domin amfanin noma bayan bukatar da jama'a s**a gabatar. Amma ya jaddada cewa an tanadi wuraren da dabbobi ke bi (cattle routes) yadda ya k**ata, don haka bai k**ata a taɓa su ba.

Saboda haka, Gwamna Bala Mohammed ya yi kira da a kwantar da hankali, yana mai cewa gwamnati za ta kafa kwamiti na musamman da zai duba dukkan rabon filaye da nufin tabbatar da adalci ga kowa da kowa.

Mutanen da abin ya shafa daga ɓangarorin biyu — manoma da makiyaya — sun bayyana irin abubuwan da ke faruwa a dazukan Yautari, Alia da sauran wurare a Darazo, inda s**a roƙi Gwamna Bala Mohammed da ya kawo musu ɗauki.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bauchi, CP Sani Aliyu, ya jinjina wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan mataki da ya ɗauka. Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro na kan lamarin, tare da gargadin jama'a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Shugabannin al’umma daga ƙaramar hukumar Darazo da s**a haɗa da 'yan majalisar jiha daga mazabar Darazo da Sade, shugaban ƙaramar hukumar Darazo, hakimin Darazo da ɗan majalisar wakilai na Darazo/Ganjuwa, Mansur Manu Soro — duk sun yaba da kokarin Gwamna Bala Mohammed tare da alkawarin ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Darazo.

Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya auri mata ta huɗu a Abuja. Hakan na nufin a yanzu ya rufe ƙofa.
07/18/2025

Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya auri mata ta huɗu a Abuja. Hakan na nufin a yanzu ya rufe ƙofa.

Injiniya Surajo Zai Ba Wanda Ya Haƙa Kabari Kyautar Naira Miliyan 1Katsina – Shugaban Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Jihar Ka...
07/17/2025

Injiniya Surajo Zai Ba Wanda Ya Haƙa Kabari Kyautar Naira Miliyan 1

Katsina – Shugaban Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Jihar Katsina, Injiniya Surajo Yazid Abukur, ya ce yana neman dattijon da ya haƙa kabarin marigayi Muhammadu Buhari domin ya ba shi kyautar Naira miliyan ɗaya.

Ya ce kuma mutum biyu da s**a taimaka wajen k**a masa wurin aikin za su samu kyautar Naira dubu 250 kowannensu a matsayin jari.

Injiniya Surajo ya ce wannan tallafi ne na girmamawa da godiya bisa irin gudunmawar da s**a bayar a lokacin jana’izar tsohon shugaban ƙasa.

" Har Ga Allah Bànyí Niyyàr Yàfiyà Ga Buhari Ba Amma Sabóda Tàusayin Dansa Yusuf Ne Yasa Wallahi  Naji Na Yafewa Mahaifi...
07/17/2025

" Har Ga Allah Bànyí Niyyàr Yàfiyà Ga Buhari Ba Amma Sabóda Tàusayin Dansa Yusuf Ne Yasa Wallahi Naji Na Yafewa Mahaifinsa Dukkan Hakkínà Dake Kàñsa Tareda Rokon Allah Ya Masa Rahama Ya Gafarta Masa"

Cewar, Rukayya Abdullahi Sokoto

MASU ZANGAZANGAR MURNAR MUTUWAR BUHARI SUN GAMU DA MUMMUNAN HAƊARI A KANODaga Wakilinmu__________A yau Litinin, wani mum...
07/15/2025

MASU ZANGAZANGAR MURNAR MUTUWAR BUHARI SUN GAMU DA MUMMUNAN HAƊARI A KANO

Daga Wakilinmu
__________
A yau Litinin, wani mummunan haɗari ya rutsa da wasu gungun masu murnar mutuwar Shugaba Muhammadu Buhari.

Kamar yadda majiyarmu ta tabbatar, wata tirela ce ta kucce, ta afka cikin gungun wasu matasa da ake zargin suna gudanar da zangazangar murnar mutuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Wani shaidar da ya gane wa idonsa yadda al'amarin ya faru, ya bayyana cewa motar ta kuɓuce wa direbanta, inda ta murƙushe ɗaya daga cikin masu zangazangar.

Haka kuma, a daidai lokacin, wata mota ta daban, wacce take ɗauke da mutum uku, ita ma haɗarin ya shafe ta.

An gano cewa dukkan matasan uku da ke cikin ƙaramar motar, waɗanda aka shaida sunayensu da Sani, Amar da Jafar, dukkansu sun rasu a nan take.
__________


Photo Credit: Dud Malumfashi

Assalamu Alaikum Masoya Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallama).Barkan Ku Da Safiya Yau Tala...
07/15/2025

Assalamu Alaikum Masoya Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallama).

Barkan Ku Da Safiya

Yau Talata 15 Ga Watan Yuli 2025.

Ranar 15 ga watan Yuli, ita ce rana ta 196 a cikin Shekara a kalandar MIladiyya; Yau ya rage saura 169, zuwa karshen shekara. Wanda yayi daidai da 20 ga watan Muharram na Shekara ta 1447, bayan Hijirar Manzo Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallama) daga Makka zuwa Madina. Yau ya rage Saura Kwanaki 218 a soma Azumin watan Ramadan mai albarka. Wanda za a fara a Ranar Talata 17 ga watan Fabrairu na shekarar 2026 In Sha Allah.

07/10/2025

I got over 2,500 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

DA DUMI-DUMI: An kore Ni daga Gidan Sarkin Kano saboda muna zuwa Gidan Nassarawa wajen Aminu Ado Bayero - Bawan Sarki
07/09/2025

DA DUMI-DUMI: An kore Ni daga Gidan Sarkin Kano saboda muna zuwa Gidan Nassarawa wajen Aminu Ado Bayero - Bawan Sarki

07/09/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abban Yusuf, Babangid Dabo, Idris Lawan Drz, Nasiru Usiman Zuntu, Sulaiman Kazeems, Usman Abdullahi Darazo, Abbas Alamin, Bello Ahmed Malala

Ahmed Musa ya jagoranci zaman farko na fahimtar juna a matsayinsa na sabon Janar Manaja na Hukumar Ƙwallon Ƙafar jihar K...
07/08/2025

Ahmed Musa ya jagoranci zaman farko na fahimtar juna a matsayinsa na sabon Janar Manaja na Hukumar Ƙwallon Ƙafar jihar Kano wato Kano Pilers tsakaninsa da shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafar Malam Ali Muhammad Umar tare da kuma sauran mambobin hukumar a jiya Litinin.

📸Kano Pillars media

🔴 AN MIKA TAKARDUN NEMAN KIRKIRAR MASARAUTAR DARAZO A JIHAR BAUCHIBabban tawaga daga karamar hukumar Darazo, a ƙarƙashin...
07/07/2025

🔴 AN MIKA TAKARDUN NEMAN KIRKIRAR MASARAUTAR DARAZO A JIHAR BAUCHI

Babban tawaga daga karamar hukumar Darazo, a ƙarƙashin jagorancin Hon. Muhammad Didado, ta mika takardun neman kafa Babban rmasarautan Darazo MAI DARAJA TA DAYA

An mika takardun ga Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Bauchi.

Takardun sun kasance na neman amincewar gwamnati wajen kafa Masarautar Darazo, tare da karin Hakimai da Gundomi Dan samar da Babban masarauta.

Wannan mataki ya biyo bayan kafa kwamitin musamman da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad (Kauran Bauchi), ya kirkiro domin karɓar bukatun al’umma masu neman ƙirƙirar sabbin masarautu a faɗin jihar.

Tawagar ta haɗa da manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki daga yankin, ciki har da Shugaban Karamar Hukumar Darazo, Hon. Sama'ila Ya'u Sade; tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Hon. Kawuwa Shehu Damina; dattawa; malamai; 'yan kasuwa; 'yan siyasa; da sauran wakilan al’umma.

Sun bayyana cewa wannan bukata ta kafa masarautar Darazo na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban yankin tare da haɗa kan al’umma baki ɗaya.

---

ME ZAKU CE KAN HAKAN.....?

Address

New G. R. A Adamawa
New York, NY

Telephone

+2349078810172

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darazo Gida posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Darazo Gida:

Share