Adam Adam

Adam Adam Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Adam Adam, Digital creator, University of Maiduguri, New York, NY.

Hausa Digital Creator 🇳🇬
💻 Fasaha • AI • Cybersecurity
🎓 Ayyuka • Scholarships • Opportunities
📱 Bayani mai amfani cikin Hausa
👇 Ka biyo shafin domin sabbin bayanai

[email protected]

Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad-Sani II, Ya Rasu Yana da Shekaru 85Mai Martaba Sarkin Gumel a Jihar Jigawa, Alhaji A...
09/03/2026

Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad-Sani II, Ya Rasu Yana da Shekaru 85

Mai Martaba Sarkin Gumel a Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Muhammad-Sani II, ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.

🇳🇬 GWAMNATIN TARAYYA TA UMARCI A MIƘA AIKIN INLAND DRY PORTS ZUWA NPAGwamnatin Tarayya ta umarci a miƙa ayyukan Inland D...
09/03/2026

🇳🇬 GWAMNATIN TARAYYA TA UMARCI A MIƘA AIKIN INLAND DRY PORTS ZUWA NPA

Gwamnatin Tarayya ta umarci a miƙa ayyukan Inland Dry Ports daga hukumar Nigerian Shippers’ Council zuwa hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, wato Nigerian Ports Authority (NPA).

Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Ruwa (Blue Economy), Adegboyega Oyetola, ne ya bayar da wannan umarni domin a samar da cikakken rabuwar ayyukan hukumomin da ke kula da tashoshin jiragen ruwa.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman, Bolaji Akinola, ya fitar, Oyetola ya kuma bada umarnin a kafa wani kwamitin ma’aikatar nan take, wanda zai kula da yadda za a sauya Nigerian Shippers’ Council zuwa sabuwar hukumar Nigeria Ports Economic Regulatory Agency (NPERA).

Wannan mataki ya biyo bayan sanya hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dokar NPERA ta shekarar 2026.

Manufar wannan sauyi ita ce kawar da cin karo tsakanin ayyukan hukumomi, tare da tabbatar da cewa kowace hukuma tana gudanar da aikin da aka ware mata.

Sabuwar dokar ta NPERA za ta samar da cikakkiyar hukuma da za ta kula da harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwa a Najeriya.

A da dai Nigerian Shippers’ Council ce ke riƙe da wannan aiki na wucin gadi tun shekarar 2014, amma yanzu za a sauya ta zuwa sabuwar hukumar NPERA.

🚨 SHAIKH ADAM ASHAKA NA NEMAN MIJI GA WATA BUDURWA DA TA KARƁI MUSULUNCIShaikh Adam Ashaka ya bayyana cewa akwai wata bu...
09/03/2026

🚨 SHAIKH ADAM ASHAKA NA NEMAN MIJI GA WATA BUDURWA DA TA KARƁI MUSULUNCI

Shaikh Adam Ashaka ya bayyana cewa akwai wata budurwa ‘yar gidan masu bautar Dodo, wadda Allah Ya shiryar da ita ta karɓi addinin Musulunci.

A cewarsa:

«“Iyayenta masu bautar Dodo ne, amma ita ta karɓi Musulunci. Ta ce a samo mata miji nagari wanda zai riƙa koya mata addinin Musulunci, ya kula da ita kuma ya riƙe ta da amana.»

«Duk wanda yake da niyyar aurenta fisabilillahi, ya tuntube ni. In shaa Allahu za mu haɗa shi da ita, amma akwai sharadin ya kasance mai haƙuri da fahimtar halayenta da dabi'unta har sai ta saba da sabuwar rayuwar da take ciki. Domin tun tana ƙarama ba ta taɓa rayuwa cikin jama'a ba, a jejin da iyayenta suke rayuwa ta taso.”»

📩 Idan kana da niyyar aure kuma kana ganin za ka iya taimaka mata wajen koyon addininta tare da kula da ita cikin mutunci, ka aiko mana da saƙo ta DM domin mu haɗa ka da Shaikh Adam Ashaka.

Allah Ya tabbatar da mu a kan shiriya. 🤲

Adam Adam

🚨 CIKIYA! CIKIYA!! CIKIYA!!! 🚨Ana roƙon taimakon jama'a domin a gano 'yan uwan wannan bawan Allah.A yanzu haka, gawarsa ...
09/03/2026

🚨 CIKIYA! CIKIYA!! CIKIYA!!! 🚨

Ana roƙon taimakon jama'a domin a gano 'yan uwan wannan bawan Allah.

A yanzu haka, gawarsa tana Magama Gumau, a Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi. An ce ya rasu ne a gefen Zawiya da ke kan hanyar Gumau, amma har yanzu ba a san 'yan uwansa ba, sannan ba a san daga inda ya fito ba.

🙏 Don Allah a taimaka a yaɗa wannan saƙo, ko Allah zai sa wani daga cikin 'yan uwansa ko waɗanda s**a san shi su gani.

Allah Ya jiƙansa, Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Amin 🤲

Mu ma idan lokacin tafiyarmu ya zo, Allah Ya sa mu cika da imani. Amin. 🤲

Kamar yadda kuke gani gobara ce ta tashi yayinda tankar dakon mai tafaɗi jama'a s**a kewayeta suna ɗibar mai. Jami'an ka...
09/03/2026

Kamar yadda kuke gani gobara ce ta tashi yayinda tankar dakon mai tafaɗi jama'a s**a kewayeta suna ɗibar mai. Jami'an kare hatsari na kan hanya sun sha jan kunne mutane idan abu makamanci haka ya faru, adaina gaggawan zuwa wajen sai an tabbatar da duk wata hanya da za'a kare dukiya da rayuka ya samu amma mutane basaji.
Jama'a ku ringa kiyaye lafiyarku da dukiyoyinku mussaman lokaci irin wannan idan ansamu hatsarin tankan mai, muna fata Allah yakiyaye gaba.

Zan saka muku videon a kwament section👇👇👇


Kubiyoni don samun updates Adam Adam

🥊🔥 SANGWAM ƊAN DAMBE — SUNAN DA YA TAƁA GIRGIZA FILAYEN DAMBE!Idan aka ambaci fitattun jaruman damben gargajiya na Arewa...
09/02/2026

🥊🔥 SANGWAM ƊAN DAMBE — SUNAN DA YA TAƁA GIRGIZA FILAYEN DAMBE!

Idan aka ambaci fitattun jaruman damben gargajiya na Arewa, akwai wasu sunaye da har yau magoya bayan dambe ba sa mantawa da su.

Sangwam Ɗan Dambe na daga cikin irin waɗannan jarumai. Kallonsa kawai za ka yi ka fahimci cewa mutum ne mai ƙarfi, jarumtaka da cikar jiki! 💪🥊

A Arewa, dambe ba wasa kawai ba ne. Al'ada ce da ta daɗe tana nuna jarumtaka, ƙarfin hali da kuma bajinta.

🔥 Amma ga tambayar masu son dambe:

Wa ya taɓa ganin Sangwam Ɗan Dambe da idonsa yana dambe a fili? 👀🥊

Idan ka san tarihinsa ko kuma ka taɓa kallonsa yana dambe, ka sauke mana labarinsa a comment! 👇

Wane ɗan dambe ne ya fi burge ka a tarihin damben gargajiya na Arewa?




Adam Adam

Duk wanda ya canki inane nan a garin kano yana da kyautar dubu ashirin 20 Adam Adam
09/02/2026

Duk wanda ya canki inane nan a garin kano yana da kyautar dubu ashirin 20



Adam Adam

Acikin hoton nan akwai wani numba a rubuce, wane  numbaA, B, C?
09/02/2026

Acikin hoton nan akwai wani numba a rubuce, wane numba
A, B, C?

Ni dai aganina physics ne.Kai fa?
09/02/2026

Ni dai aganina physics ne.
Kai fa?

Address

University Of Maiduguri
New York, NY
600230

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Adam Adam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Adam Adam:

Shortcuts

Share