
09/17/2025
TARIHI
A ranar 17 ga Satumba, 2006, wani jirgin sama na Sojin Sama na Najeriya (Dornier 228) ya yi hatsari a Jihar Benue yayin da yake kan hanyarsa zuwa taron Sojin Kasa a Obudu Cattle Ranch, Jihar Cross River.
Aƙalla mutane 13 daga cikin 17 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu, ciki har da manyan janarori 10. Sun tafi taro don tattaunawa kan manufofin da za su tsara makomar soji da ƙasar baki ɗaya. Hatsarin ya faru ne sakamakon munanan yanayi, kuma jirgin ya bugi wani dutse.
Sojoji huɗu kawai s**a tsira. Wannan babban rashi ne ga ƙasa a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo, wanda ya katse ziyarar aikinsa daga Singapore don komawa gida saboda wannan bala’i.