18/07/2025
Zunubai da tasirin su
Zunubai suna iya jawo ƴan uwan su zunubai.
Yana daga cikin illolin zunubai shine:suna jawo wasu Zunuban,kamar yadda kyawawan ayyuka suke jawo irin su,wannan ya sa in dá mai laifi zai bar aikata saɓo, dá zuciyar sa ta yi masa ƙunci, ba zai samu jin daɗi ba,har sai ya dawo zuwa ga Zunuban, akwai waƴan da ko sun aikata saɓo ba sa jin daɗi,amma suna yi ne saboda zafin da suke ji in ba su aikata saɓon ba.
Akwai wani mutum da kullum sai ya sha karan sigari(cigarettes/Tába) masu yawa,sai aka tambaye shi dalili, sai ya ce: ai sai ya sha yake samun natsuwa, sai aka ce dashi,ya dinga yin zikiri mana maimakon sigarir, tunda Allah ya ce:الذين ءآمنو وتطمئن قلوبهم بذكرالله ma'ana:waƴanda s**a yi imani da Allah suna samun natsuwa da ambaton Allah, amma da alama ɗabbaƙa hakan zai yi masa wahala(ƙila sakamakon wancan zunubin)
Bawa ba zai gushe ba yana aikata ayyukan alheri har sai Allah ya aiko da mala'ikun rahama sun ƙarfafe shi,
Bawa ba zai gushe ba yana aikata ayyukan zunubi ba har sai Allah ya aiko masa shaiɗanun da za su ƙarfafe shi,su kuma ƙawata masa Zunuban..
Allah ya kiyaye mu da aikata zunubai.
Prof Jameel Yusuf Zarewa.