11/06/2026
Ma’aikatan gwamnati su ne manyan ginshiƙan gudanar da ayyukan ƙasa, inda da dama daga cikinsu ke shafe shekaru masu yawa suna hidimtawa al’umma da ƙasa har zuwa lokacin ritayarsu.
Bayan kammala aiki, wasu ma’aikata na fuskantar ƙalubale kamar tsadar rayuwa, rashin isasshiyar kulawar lafiya, da wahalar daidaita rayuwa ba tare da albashi na wata-wata ba, duk da irin gudunmawar da s**a bayar a tsawon shekarun aiki.
Wannan babban ƙalubale ne da ke tayar da muhawara, tare da kira ga gwamnati da ta fito da kyakkyawan tsari mai inganci wanda zai kare mutuncin waɗanda s**a kammala aikin gwamnati tare da tabbatar da jin daɗinsu bayan sun bar aiki.
Shin a ganinku Gwamnati na da wani shiri na musamman domin kula da ma’aikata bayan ritaya?
Muna maraba da saƙonnin ra'ayoyinku kan wannan batu domin karantawa a cikin Labaranmu.