05/05/2025
๐๐๐๐ RUฤANI ๐๐๐๐
NA
FATIMA ฤAHIRU FUNTUWA BINTA
Page 31
Nayi murmushi cike da jin daฤin waฤan nan kalamai nashi, nace "Alhaji Mansur idan da sabo na saba da irin wannan koฤawar taka, amma koda yaushe kake karanto minsu, sai in jisu tamkar sababbi, in kasance cikin jin daฤi da fara'a, sai in tsinci kaina ina mai yin murmushi, idan kana yimin irin waฤan nan kalaman, kuma koda cikin 'bacin rai nake, da zarar kazo shikenan ka wanke shi, nagode ma Allah da yayi haฤuwa ta dakai, ya mallakamin kai a matsayin muji na, koba komai nasan zan kasance cikin farin ciki na har abada, samun jajurtaccen namiji mai sauya tunanin 'ya mace a lokaci guda, wannan babbar nasara ce a wurin kowace mace, sannan babban cikan buri na, gashi zan gama rayuwata ni kaฤai a wurin namiji, k**ar kai, wannan wani abin al-fahari ne a wuri na, yadda na tashi a gidan mu ni kaฤai na samu gata, haka zan rayu a wurin muji na ni kaฤai ba tare da gatan ya goce mani ba."
Ya ce "Ta yaya za'ayi mace k**arke a haฤa soyayyar ta da wata? Idan namiji ya aikata hakan tamkar yayima kanshi gi'bi ne, kin gane abinda nake nufi? Idan mutum ya haฤa ki da wata, to duk ranar daya yanke wasu kwanaki don ya kaima abokiyar zaman ki, tamkar ya yanke ma kanshi wani jin daฤi ne, ya tauye kanshi sosai a wannan rana."
Har cikin kaina naji wannan maganar tayimin yawo, ya wani 'kara tsuma ni, ina jin kaina lallai ni wata ce ta daban.
Nace "Ina son ka MANSUR."
Ya ce "Nima ina son ki Amina."
Muka gama firar, sannan ya fito motar ya shiga tashi ya tafi.
Munyi Aure da Alhaji mansur, irin auren soyayyar dana saki jiki da shi, akan lallai ba wata sai fa ni ฤin, k**ar yadda kullun yake 'kara shaida mani.
Shekarata Talatin da biyar dashi a yanzun haka, haihuwata bakwai tare da shi, ina cikin jin daฤi da kwanciyar hankali sosai, kuma arzi'kin mu koda yaushe 'kara gaba yake, don yanzun Mansur ya fita daga 'kar'kashin A