Taskar Arewa TV

  • Home
  • Taskar Arewa TV

Taskar Arewa TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Taskar Arewa TV, Video Creator, .

Taskar Arewa TV dandali ne na yada sahihan labarai, al'adu, ilimi, da abubuwan da s**a shafi ci gaban al'umma, domin isar da muryar Arewa zuwa ga duniya baki ɗaya.

SANARWA TA MUSAMMANAna sanar da al'umma cewa a ranar 20 ga wannan wata, mutane 150 za su amfana da tallafin man fetur ky...
09/06/2026

SANARWA TA MUSAMMAN

Ana sanar da al'umma cewa a ranar 20 ga wannan wata, mutane 150 za su amfana da tallafin man fetur kyauta (Free Fuel) daga Dan Hutu Foundation, ƙarƙashin jagorancin Dan Hutu M.A. Danhutun Dan Amana.

Masu mashina 100 za su karɓi man fetur na Naira 3,000 kowannensu.
Masu Keke Napep 50 za su karɓi man fetur na Naira 4,000 kowannensu.
Allah Ya sanya alheri a cikin wannan shiri, Ya kuma saka da alkhairi ga masu tallafawa.

Karamar hukumar Toro jihar Bauchi Nijeriya.
Dan Hutu M.A. Danhutun Dan Amana

Taskar Arewa Tv

Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a siyasar Najeriya, Rotimi Amaechi, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa an ba shi tik...
09/06/2026

Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a siyasar Najeriya, Rotimi Amaechi, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa an ba shi tikitin mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, yana mai cewa babu wanda ya taɓa neman ya tsaya takarar saboda sun san “ƙimarsa” da irin martanin da zai bayar.

Amaechi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC.

Tsohon gwamnan Rivers ɗin ya ce ya gana da shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, amma ya jaddada cewa ba su tattauna batun tikitin mataimakin shugaban ƙasa ba.

“Kafin a fitar da sanarwar, mun yi shawarwari tare. Amma babu wanda ya taɓa cewa in tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa domin sun san ƙimata da martanin da zan bayar,” in ji Amaechi.

Ya kuma yi watsi da sak**akon zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na ADC, yana zargin an tafka maguɗi tare da hana wasu masu zaɓe damar kaɗa ƙuri’arsu.

Amaechi ya bayyana cewa matsayar ƙarshe da aka cimma kan rikicin ta kasance tsakaninsa da ɗan takarar jam’iyyar, Hayatu-Deen, wanda shi ma ya nuna rashin amincewa da sak**akon zaɓen.

Kalaman nasa sun sake janyo sabuwar muhawara a siyasar Najeriya, musamman yayin da ake ta rade-radin haɗakar manyan ‘yan siyasa gabanin zaɓen 2027.

Masu sharhi na ganin furucin Amaechi na nuna cewa har yanzu yana kallon kansa a matsayin babban ɗan takarar shugabanci, ba mataimaki ba.

Sai dai tambayar da mutane da dama ke yi yanzu ita ce: Shin Amaechi na shirya wata babbar tafiya ta siyasa a 2027, ko kuwa wannan martani ne kawai don kare martabarsa a siyasa?

Taskar Arewa TV

Kiyi comment da raayoyinku...
Kiyi like da kuma share...

𝗚𝗮𝘄𝘂𝗻𝗮 𝘀𝗲𝗲𝗸𝘀 𝗔𝗗𝗖 𝗴𝗼𝘃 𝘁𝗶𝗰𝗸𝗲𝘁 𝗮𝘀 𝗱𝗲𝗳𝗲𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻 𝘁𝗮𝗹𝗸𝘀 𝗮𝗱𝘃𝗮𝗻𝗰𝗲 : Dr. Nasiru Gawuna, former APC candidate, is in advanced talks t...
09/06/2026

𝗚𝗮𝘄𝘂𝗻𝗮 𝘀𝗲𝗲𝗸𝘀 𝗔𝗗𝗖 𝗴𝗼𝘃 𝘁𝗶𝗰𝗸𝗲𝘁 𝗮𝘀 𝗱𝗲𝗳𝗲𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻 𝘁𝗮𝗹𝗸𝘀 𝗮𝗱𝘃𝗮𝗻𝗰𝗲 :

Dr. Nasiru Gawuna, former APC candidate, is in advanced talks to join the African Democratic Congress (ADC) and secure its 2027 governorship ticket.

The 2023 governorship candidate of the All Progressives Congress in Kano State, Dr Nasiru Gawuna, is set to dump the Nigeria Democratic Congress for the African Democratic Congress following ongoing negotiations between both parties.

Findings by our correspondent revealed that discussions between Gawuna’s camp and the ADC leadership in Kano had reached an advanced stage, with both sides expected to hold a final meeting on Monday to conclude the arrangement.

The Kano State chairman of the ADC, Musa Ungogo, confirmed the development in an exclusive interview with The PUNCH on Monday, saying Gawuna initiated the talks through emissaries who met with the party leadership over the weekend.

Ungogo dismissed claims circulating on social media that the ADC was courting the former deputy governor, insisting that the move came from Gawuna and his associates.

The story being circulated that the ADC approached Gawuna is not correct. It was Gawuna who approached us. He sent a delegation to meet us, and discussions have been ongoing since then,” he said.

According to the ADC chairman, Gawuna’s delegation included a former Chairman of Kumbotso Local Government Area, Alhaji Sagir Fanshekara, and Hon Kadawa.

He said the delegation met with him and the party’s state secretary on Saturday as part of efforts to negotiate the terms of Gawuna’s entry into the party.

Taskar Arewa Tv
Follow, like and share for more legit news

"Nima Danake Shekara 66, Dole Na Kirawo Dan Shekara 63 Yaro.Balantanama Kuma Dan Shekara 69, Wanda Ya Temaki Rayuwar Ka ...
09/06/2026

"Nima Danake Shekara 66, Dole Na Kirawo Dan Shekara 63 Yaro.
Balantanama Kuma Dan Shekara 69, Wanda Ya Temaki Rayuwar Ka Tun Kana Dan Shekara 21 A Duniya, Yake Temakon Rayuwar Ka."

— Cewar Aminu Abdussalam Gwarzo (Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano)

Taskar Arewa Tv

Meye raayinku game da wannan furuci??
Ku saka mana a comment section...

SUBHANALLAHI: Daya daga cikin dattawan da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi, Malam Yahaya Billi, ya rasu a hannun masu ...
09/06/2026

SUBHANALLAHI: Daya daga cikin dattawan da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi, Malam Yahaya Billi, ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.

Ƙungiyar Izalah JIBWIS reshen Ƙaramar Hukumar Koko-Besse ta sanar da rasuwarsa, tare da bayyana cewa an gudanar da Sallar Jana'izar Ga'ib da ƙarfe 4:30 na yammacin yau a ƙofar gidan Sarkin Koko.

Taskar Arewa Tv

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wata mata da ake zargi da kashe uwargidan mijinta a unguwar Gwarg...
06/06/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wata mata da ake zargi da kashe uwargidan mijinta a unguwar Gwargwaje da ke Zaria, bayan ta soka mata wuƙa har lahira.

Rahotannin aka tabbatar daga kakakin rundunar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne sak**akon rikici tsakanin matan gidan, inda daga bisani ita amaryar ta kai wa Uwargidan s**a da ya yi sanadin mutuwar ta.

Jami’an tsaro sun ce an k**a wadda ake zargin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya jawo rikicin da kuma tabbatar da hukunci da ya dace.

Taskar Arewa Tv

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da rage kuɗin hayar tarakta ga manoma daga Naira 100,000 zuwa Naira 50,000 ...
06/06/2026

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da rage kuɗin hayar tarakta ga manoma daga Naira 100,000 zuwa Naira 50,000 domin ƙarfafa noma da bunƙasa samar da abinci a fadin jihar.

Taskar Arewa Tv

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta sanar da sabon tsarin “Prosumer” da zai bai wa masu amfani da solar damar ...
06/06/2026

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta sanar da sabon tsarin “Prosumer” da zai bai wa masu amfani da solar damar sayar da wutar da ta wuce bukatarsu ga kamfanonin rarraba wutar lantarki ta Najeriya.

Me zaku ce?

Taskar Arewa Tv

05/08/2024

Intent trade yana da kyau sosai. Ya k**ata ku gwada.

Wadannan hotuna da kuke gani, an dauke su ne a 2011 lokacin da ake gudanar da 'protest' a kasar Egypt domin kawar da Shu...
05/08/2024

Wadannan hotuna da kuke gani, an dauke su ne a 2011 lokacin da ake gudanar da 'protest' a kasar Egypt domin kawar da Shugaba Hosni Mubarak da ya shafe sama da shekaru 30 a kan karagar mulki. Abun sha'awa a nan shine, ba su yi irin abubuwan da mutanen mu suke yi ba.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Arewa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Taskar Arewa TV:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share