25/07/2025
Hukumar ta Bude bangaren Amsar korafin Al,umma domin tsabtace Aikin,
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Jihar Katsina (KASSAROTA) karkashin Jagoranchin D,G Yahaya Garba Garba ta kirkiro Sabon sashen kula da korafe korafen Al'umma. Sashen wanda yake karkashin ofishin Jami'in Hulda da Jama'a na Hukumar, zai yi aiki don karbar korafe korafen Al'ummar Akan yanda jami'an Hukumar suke gudanar da ayyukansu, matsalolin cin hanci da rashawa, amfani da karfi ko matakan da basu dace ba na tursasawa al'umma, ko rashin bin ka'idojin aiki a yayin gudanar da ayyukansu.
Kuma zaku iya kawo shawarwarin akan yanda za,a inganta ayyukan hukumar don tsare lafiya da dukiyoyin al'ummar Jihar Katsina. Wannan mataki yana daga cikin sabbin Matakan da Gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta dauka domin inganta ayyukan hukumar da kare mutuncin al'ummar Jihar Katsina,
Kafa sashen na da nufin rage yawan korafe korafen al'umma akan cin zarafi, cin hanci da rashawa, ko sanya karfi da ya wuce ka'ida a yayin gudanar da ayyukan jami'an.
Sashen zai rika gudanar da bincike don tabbatar da sahihancin korafe korafen da kuka kawo kafin daukar matakin da ya dace akan Jami'an da abin ya shafa abunda muke bukata Ku kawo kwararan sheda ko sahihiya,
Hukumar tana Kara kira ga al'ummar Jihar Katsina musamman masu amfani da ababen hawa, da su kiyaye dokokin tukin da aka gindaya domin kare lmutunchin su ,Lafiyarsu da dukiyoyin su
daga Karshe Hukumar tana Kira ga masu ababen hawa da su cika dukkan ka'idojin da dokar kasa ta kayyade, tare da kiyaye dokokin hanya a matsayin Ka na Dan kasa Nagari domin guduwa tare da tsira tare
Mustapha Ibrahim Kofar Marusa
Media Assistant to Katsina state
Governor ministry of Works
Housing and Transport.