TYDA

TYDA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from TYDA, Film/Television studio, Opp. Shafa Felling station sectaria Street Arhan_kunuMubi, Mubi.

Wannan shafin yana kawo muku sahihan labarai ne dasuke faruwa aduniya da kuma bangaren addini da al'adu kasar hausa kuci gaba da bibiyarmu zamuna kawo muku abubuwa daban-daban na ilimi da rayuwa

28/03/2025
Rugum Babban Motsi...Yadda Mai Martaba Sarkin Zazzau Ya Jinjina ga Jama'ar wajen  garin Zariya... Yayin Ziyaran bazata a...
25/03/2025

Rugum Babban Motsi...

Yadda Mai Martaba Sarkin Zazzau Ya Jinjina ga Jama'ar wajen garin Zariya... Yayin Ziyaran bazata ana tsaka da Rufe karatun Tafseer na Young Sheikh Zaria wanda ya gudana a yau dinnan a Zawiyyar Maulana Sheikh Aliyu Maiyasin Zaria...

Yadda garin ya cika maza da mata yara da manyan sunji dadin ganin Mai Gari kuma sun masa Addu'an Allah Yaima Sarki Jagora! Amin.

GA WANI LABAR: Wannan hoton yana nuna surar Nisha Ghimire, wadda ta kasance matashiya ta biyu Mafi kyawu a gasar Miss Wo...
23/12/2024

GA WANI LABAR: Wannan hoton yana nuna surar Nisha Ghimire, wadda ta kasance matashiya ta biyu Mafi kyawu a gasar Miss World ta Ƙasar Nepal.

Hoton farko (dama) an dauka ne kuma aka dora shi a Instagram ranar 14 ga Satumba, 2019, yayin da hoton na biyu (hagu) aka dauka ranar 8 ga Yuni, 2021 a asibitin Norvic. Abin mamaki, duk Mace ɗaya ce dai Nisha Ghimire - Ƴar Ƙasar Nepal.

A shekarar 2018, Nisha tana tsaka da ganiyarta da shahararta Wajen Kyawu da Ƙoshin Lafiya inda take Samun Manyan Kuɗaɗe daga tallan da Kamfanunuwa ke bata na Kayan Kwalliya da Mai na shafawa da sauran Ƙawa da ado Kasancewarta Ta biyu Mafi Kyawu a Ƙasar Nepal da Kuma Karɓar Kuɗaɗe daga Kamfanunuwa da s**a ɗauketa a Matsayin jakadiyarsu.

Kamfanoni suna tururuwa don sanya ta a matsayin jakadiyar su. fitattun mutane daga Nepal da Indiya, daga sassan duniya , suna neman Ƙulla alaƙa da ita.

Ƙaddara ta riga Fata , a watan Janairu 2019, lokacin da ta tafi Dehradun, a ƙasar Indiya don kara kwarewar ta a harkar fim da tallan kayan kwalliya, kaddara ta zo mata da wani tsari na daban. Rashin Lafiya ta Kamata Kwatsam Wadda aka kasa Gano Kanta b***e asan maganin da za a bata don warkar da cutar {kamar yadda jaridun Ƙasar s**a ruwaito}.

Iyalan ta sun kashe Maƙudan Kudaɗen da ta tara a asusunta (Bank) don yi Mata Magani amma abu yaƙi sauƙi , duk abokan sharholiyarta dake Rayuwa tare da ita S**a Fece Kamar ɗaukewar ruwan Sama, kuma Shahararta da ɗaukakarta s**a ƙare nan take. Aka dawo da ita Ƙasar Nepal daga Ƙasar indiya don jiran ajalinta.

Abokan ta da Ƙawayenta suna zuwa ne kawai Duba ta don su ɗauki hotuna tare da ita kuma su yi Posting a Media su don samun "likes", ba da niyyar tausaya mata ko taimaka mata ba yayin da take kwance zafin ciwo da Talauci yana addabarta.

Ƴan siyasa, abokanta Ƴan wasan Kwaikwayo, da dukan Masu nuna mata So Duk S**a ɓace kamar Ƙasa ta haɗiye su.

An rawaito cewa Mahaifiyarta tace " idan aka fito da ita Falo aka kwantar akan babbar kujerar dake Saitin T.V Idan tsausayi

Gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar gurfanar da aminan dan bindiga Bello Turji su takwas da ma shi kansa da yanzu haka a...
23/12/2024

Gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar gurfanar da aminan dan bindiga Bello Turji su takwas da ma shi kansa da yanzu haka ake nema ruwa jallo

Ƴan bindiga sun kashe basarake tare da sace matarsa a KwaraƘarinbayani - https://bbc.in/3HKJ3VE
02/02/2024

Ƴan bindiga sun kashe basarake tare da sace matarsa a Kwara

Ƙarinbayani - https://bbc.in/3HKJ3VE

Rundunar mai suna Askarawan Zamfara ta ƙunshi zarata 2,646, waɗanda aka harhaɗa daga ƙananan hukumomin jihar 14, kuma su...
31/01/2024

Rundunar mai suna Askarawan Zamfara ta ƙunshi zarata 2,646, waɗanda aka harhaɗa daga ƙananan hukumomin jihar 14, kuma sun samu horo na musamman daga jami'an tsaro da ƙwararru daban-daban a fannin tsaro.

Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatin jihar na amfani da hanyoyi da dabaru daban-daban wajen yaƙi da miyagun laifuka a jihar.

Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar canji ta Abuja, Alhaji Abdullahi Dauran, wanda ya sanar da hakan a wani taron manema laba...
31/01/2024

Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar canji ta Abuja, Alhaji Abdullahi Dauran, wanda ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a Najeriya.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/3SjrCk0

Wasu Daga Cikin Manyan Kadarori Da EFCC Ta Samu  Daga Hannun Ministar JIN_ƘAI Betta Edu, Mai Suna (WAKE ƊAN WURI).Owners...
15/01/2024

Wasu Daga Cikin Manyan Kadarori Da EFCC Ta Samu Daga Hannun Ministar JIN_ƘAI Betta Edu, Mai Suna (WAKE ƊAN WURI).

Ownership of an estate at Linda Chaulker Road, Asokoro Extension worth N750 million.

Plaza at El-Rufai Crescent Guzape Asokoro Extension worth N1.4 billion.

One filling station along Abuja-Kubwa Express way, worth N1.2 billion.

Ownership of four (4) estates at Metropolitan Estate Abuja worth N350 million.

Six (6) plots of land in airport road Abuja worth N300 million.

Four (4) estates at airport road worth N530 million.

Two (2) estates in Federal Housing Estate Calabar Cross River State worth N190 million.

One (1) Dillion station in Calabar metropolis worth N430 million.

Cash Discovered by the EFCC

N2.7 billion in Zenith bank
N725 million in First bank
N388 million in Polaris bank
$2.1 million in Zenith bank
£57,000 in zenith bank
€13,000 in zenith bank
$6500 in Polaris bank

Yanzu haka hukumar tana ci-gaba da tattara kadarorinta da s**a haɗar da gwala-gwalai da sauran sarakuna masu daraja

Source: Nah Seeyr

Naɗin nasa na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma'a. Ali Nuhu...
13/01/2024

Naɗin nasa na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma'a.

Ali Nuhu dai ya yi fice a harkar fina-finai a Kannywood da Nollywood.

A Ranar Juma'a Kotu Zata Raba Gardama Tsakanin Abba da GawunaLauyoyin kowace jam'iyya dai na da kyakkyawan fata na nasar...
11/01/2024

A Ranar Juma'a Kotu Zata Raba Gardama Tsakanin Abba da Gawuna
Lauyoyin kowace jam'iyya dai na da kyakkyawan fata na nasara a wannan sharia'a da za ta kawo karshen gardama da jam'iyyun biyu s**a shafe watanni suna yi a kan wannan shari'a.

Kalli yadda ƴan wasan Super Eagles s**a sha kwalliya yayin tafiyarsu zuwa ƙasar Ivory Coast inda za su wakilci Najeriya ...
11/01/2024

Kalli yadda ƴan wasan Super Eagles s**a sha kwalliya yayin tafiyarsu zuwa ƙasar Ivory Coast inda za su wakilci Najeriya a gasar AFCON 2023.

📸 - Ahmed Musa/Troost Ekong/Super EaglesNG/X

Address

Opp. Shafa Felling Station Sectaria Street Arhan_kunuMubi
Mubi
07062269828

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TYDA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TYDA:

Share